An Gudanar da Gagarumin Maulidin Sayyida Zahra (A.S) a Garin Bomo, Zariya


Daga Bashir Adam Bomo

A ranar Litinin, 15 ga Disamba, 2025, ƴan uwa Almajiran Jagoran Harkar Musulunci, Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na Majalisin Bomo, dake Karamar Hukumar Sabon Gari, Zariya, sun gudanar da gagarumin Maulidin Sayyida Fatima Zahra (A.S), ‘yar Manzon Allah (S).

An buɗe taron ne da addu’a daga bakin Malam Muhammad Barau Samaru, sannan aka yi karatun Alƙur’ani Mai Girma wanda Batula Saleh ta gabatar.

Daga bisani, Zahra’u Kabiru Bomo ta gabatar da takaitaccen jawabi kan matsayi da darajar Sayyida Zahra (A.S) a Musulunci, yayin da Mardiyya Sa’idu ta karanta Ziyarar Sayyida Zahra (A.S).

Haka kuma, Malam Mansour Samaru ya yi nasa jawabi a takaice kan martabar Sayyida Zahra (A.S), kafin zuwan babban baƙon taron.

Babban baƙon mai jawabi, Sheikh Abdulhamed Bello, ya fara jawabinsa da godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki, inda ya bayyana cewa irin wannan Maulidi hanya ce ta kusantar Manzon Allah (S), sakamakon ƙauna da muminai ke nuna masa.

Shehin Malamin ya jaddada cewa Manzon Allah (S) yana matuƙar ƙaunar Sayyida Zahra (A.S), kamar yadda ita ma take ƙaunar mahaifinta, don haka son Sayyida Zahra (A.S) wajibi ne ga muminai.

Ya ƙara da cewa Sayyida Zahra (S. A) ta yi koyi da mahaifiyarta Sayyida Khadija (A.S) wajen kula da Manzon Allah (S), abin da ya sa Annabi (S) ke kiranta da “Ummu Abiha”.

Shehin Malamin ya bayyana cewa Sayyida Zahra (A.S) ta sha wahala tun tana ƙaramar yarinya wajen kare mahaifinta daga zaluncin kafiran Makka, inda ta kasance garkuwa da kariya gare shi. Har zuwa aurenta da Imam Ali (A.S) da kuma renon ‘ya’yanta, ta nuna tarbiyya ta gari wadda babu kamarta.

An kammala taron cikin nutsuwa da tsari, tare da addu’o’in neman albarka da zaman lafiya.





 

Post a Comment

Previous Post Next Post