Daga Bello Hamza, Abuja
Sheikh Muhajjadina Sani Kano ya bayyana cewa, barazanar Amurka na kawo wa Nijeriya harin soja abu ne da ba zai yiwu ba saboda in har akwai masu ilimin taurari da bayin Allah masu ibada, saboda tsananin addu’o’i da masu ilimin taurari yi a kullum. A kan haya ya nemi ‘yan Nijeriya su kwantar da hankalinsu.
Sheikh Muhajjadina wanda shi ne shugaban masu ilimin taurari da yankin Afrika kuma mai sharhi a kan al’murran yau da kullum ya yi wannan bayanin en a tattaunawarsa da manema labarai a Abuja. Ya qara da cewa, bayanan Trump ya nuna irin tsananin jahilcinsa a kan abin da ke faruwa a Nijeriya, “Domin ainihin wuraren da waxannan rikice-rikicen suka ta’azzara yankuna ne da al’ummar Musulmai suka fi yawa kuma kowa ya sani cewa musulmai ne aka fi hallakawa a rikice-rikicen da ke faruwa a Nijeriya,” in ji shi.
Ya kuma gargaxi Amurka a kan shirinta na kawo hari Nijeriya, ya ce, duk da cewa, Amurka na gadara da qarfin makamai amma ya kamata su fahimci cewa, Nijeriya nada qarfin malamai da masu ilimin taurari wanda ba za mu yarda su samu nasarar wannan munmmunan shirin ba. Kuma mun yi bincike na musamman mun kuma gano cewa, wannan shirin ba zai tava faruwa ba. Domin haka ya nemi al’ummar Nijeriya su kwantar da hankalinsu domin wannan shirin ba zai tava faruwa ba.
Sai kuma ya nemi shugabannin Nijeriya su tsayu wajen kusantar masu ilimin taurari da bayin Allah masu bautarsa ta yadda za a ci gaba cin gajiyar baiwar da Allah ya basu. Ya kuma nemi shugabannin qasa su jagoranci ci gaba da yi wa qasa addu’ar kariya daga dukkan sharri na cikin gida dana qasashen waje, “Domin Nijeriya na da abubuwa da dama da ake yi mata hassada da su a sassan duniya. Na farko Allah ya bamu yalwan arziki ya kuma bamu zaman lafiya, wannan abu ne da wasu qasashen ba za su so ba.”
Daga nan kuma Sheikh Muhajjadina ya yi kira ga shugabanni da su qara azama wajen ganin an kawo qarshen dukkan wani tashe-tsashen hankulan da ake fuskanta a Nijeriya, “Dole a yi abin da ya kamata wajen daqile dukkan ayyukan ‘yan ta’adda ta hanyar haxa hannu da masu ilimin taurari da malamai da dukkan masu ruwa da tsaki a qasa, ta haka al’umma za su samu kwanciyar hankali.
Haka kuma ya ce, dole a dakatar da dukkan zubar da jinin da ake yi a sassan qasa ba tare da nuna bambancin addini ko qabilanci ba.
Ya kuma yi wa ‘yan Nijeriya albishirin cewa, in Allah ya yar za a fita daga dukkan matsalolin tsaron da ake fuskanta kuma komai zai dawo daidai. Ya kuma ce, bincikesu ya nuna cewa, wannan shiri na Amurka ba zai samu nasara ba, kuma ba za su iya kawo harin da suke iqirarin cewa za su kawo ba da yardar Allah.

Post a Comment