Hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), ofishin Yola, ta jagoranci aikin nemo waɗanda abin ya rutsa da su, ceto da kuma kwashe jama’a bayan ambaliyar ruwan kwatsam da ta shafi kauyuka 13 a cikin kananan hukumomin Yola ta Arewa da Yola ta Kudu a ranar Talata.
Rahotanni sun nuna cewa ruwan sama mai ƙarfi ya haddasa ambaliyar, wanda ya tilasta hukumar NEMA tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro da na agaji gudanar da ayyukan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyi.
Hukumar ta kuma shawarci mazauna wuraren da abin ya shafa da su guji komawa gidajensu har sai an tabbatar da tsaron lafiyarsu.
Post a Comment