ZAMAN JUYAYIN SHAHADAR IMAM JAFAR ASSADIK (AS) A GARIN BOMO


Daga Mardiyya Kabiru

Yan'uwa Almajiran Sayyid Ibrahim Yaqub Alzakzaky (H) na Garin Bomo suka gabatar ga Zaman Juyayi na daya daga cikin jikokin Manzon Allah wato Imam Jafar Assadik (AS) a muhallin Fudiyya Bomo.  Bayan bude taro da addua zaman ya samu halartan manyan mutane ciki harda yan'uwanmu yan Ahlulzikir Malam Aliy Dalhat da Na'ibin Bomo.

Babban malamin daya samu halartan wajen zaman shine Sheikh Umar Salisu Funtua inda wakilin yan'uwa na garin malam murtala muhammad ya gabatar dashi. Ya fara magana ne akan tin bayan hajjin bankwana da Manzon Allah(S) inda ya nasabta wasiyinsa iman ali a matsayin kalifansa tin daga lokacin iyalan annabi suka fara fuskanta hujumi daga wajen mutanen zamaninsu. Sannan ya kara da magana akan yadda iman Jafar Assadik(A S)  da mahaifinsa Iman Muhammad Albaqeer(A S) sukai rayuwa tsawan lokaci tare. Sannan ya kare maganar  tashine da yadda azzalumai zamanin suka shahadantar da iman din kadan kenan daga cikin jawabin da malamin yayi. Daga karshe na'ibin bomo shine ya rufe zaman da addua.


 

Assalamu Alaika Ya Jafar Assadik(AS).

Post a Comment

Previous Post Next Post