Kishin al'umma ya kare a zukatan 'yan siyasar Nijeriya - Bafarawa



Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ce kishi da gwagwarmayar dimokuraɗiyya ya mutu a zuƙatan 'yansiyasar ƙasar, kuma a halin yanzu sun kama hanyar hallaka dimokraɗiyya.

Attahirun Bafarawa na wadannan tsokaci ne a lokacin tattauna da BBC kan halin da kasar ke ciki.

Ya ce akwai matukar damuwa ganin yadda ake samun mutuwar adawa a fagen siyasar ƙasar saboda fifita buƙatun kai.

Sannan ya ce matuƙar aka bar lamura suka cigaba da tafiya a haka, zai iya zama babban nakasu ga makomar al'umma da ma ta ƙasar gaba ɗaya.

Tsohon gwamnan ya yi zargin cewa duk wannan sauya sheka da 'yansiyasar na bangaren hamayya ke yi suna tafiya jam'iyya mai mulki ba don komai suke yi ba na amfanin talaka, face don kansu suke yi, saboda haka ya ce siyasar hamayya ta mace a kasar a yanzu - babu akida.

Ya bada misalai da galibin 'yan siyasa da gwamnonin arewa da ya ce duk bukatun kansu suke bai wa muhimmanci, ba wai ciyar da al'umma da raya kasa ba.

'Arewa na cikin hali na koma-baya'

Tsohon gwamnan da ke nuna matukar takaici da halin da siyasar kasar ke ciki, ya ce yanzu zabi na hannun talakawan ƙasar tunda kowa na ganin yanayin da ake ciki. Kuma kamar yada bahaushe ke cewa jiki magayi.

Ɗansiyasar ya ce yankin Arewa yana cikin wani mawuyacin hali na koma-baya.

Ya ce duk inda ka ci mutum da yakin ilimi ka jefa masa jahilci to ka gama da shi.

Sannan tsohon gwamna ya ce ba zai daina fadin gaskiya ba, domin babu wanda ya ware daga halin da Najeriya ta tsinci kanta.

Tsohon gwamnan na Sokoto ya ce, yanda siyasar Najeriya take ciki a yanzu abin ya wuce saninsu.

Kuma ya ce zaben 2027 lokacin ne da masu hankali za su yi amfani da shi wajen raba kasa da tsakuwa.

Bafarawa ya ce ba zai ce komai kan gwamnatin Tinubu ba, sai dai ido ba mudi ba amma ya kasa kima, sannan ya tunasar da irin gwagwarmayar su Sardauna da sadaukarwasu wajen ganin su raya Najeriya musamman Arewa.

A watan Janairun wannan shekara ta 2025, Attahiru Bafarawa ya fice daga PDP.

Ya ce ya dauki mataki ne, wanda na ƙashin kaina ne kuma ba mai sauƙi ba, ya ɗauke shi ne sanadiyyar mayar da hankalin da ya yi kan wani sabon babi na aiki na daban, wanda ya yi daidai da manufarsa ta bunƙasa al'umma ta hanyar ƙarfafa matasa."

Duk da cewa PDP ita ce babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, ana ganin cewa rikice-rikice na cikin gida ya yi mata tarnaƙi, ta yadda ba ta iya sauke nauyin da ke kanta na sanya ido kan lamurran gwamnati mai ci ƙarƙashin jam'iyyar PAC.

A baya-bayan nan, Bafarawa ya bayyana aniyarsa ta daina tsayawa takara ko kuma karɓar duk wani muƙami na siyasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post