Jagora (H) Ya Ja Hankalin ‘Yan Uwa Akan Kyautata Ɗabi’u

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

Da yake gabatar da jawabin rufe taron karawa juna sani wanda Dandalin Dalibai da Dandalin ‘Yan’uwa mata na Harkar Musulunci suka gabatar, a ranar Lahadi 13/4/2025 a garin Kano, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky ya jaddada bukatarsa na ganin tarbiyar ‘yan uwa ya inganta.

Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa: “A kullum nakan ce, idan muka lura da su ‘yan uwa da suke kira (zuwa ga tabbatan addini), to in ma da abinda yake bani takaici, shi ne in ga su ba su siffanta da abinda suke kira akai ba. Ko kuma in ga cewa sun yi kama da mutanen da suke ce ma su gyaru.” 

Ya kara da cewa: “Idan mutum yana kokarin gyara mutane, sai ya zama shi ma bai gyaru ba, to babu gyaran kenan, domin dole ne gyararre ke kira ga gyara wasu, in shi bai gyaru ba, saura ba za su gyaru ba.”

Ya jaddada cewa: “In na ga dabi’un ‘yan kasar nan a tare da ‘yan uwa, sai in ga to meye bambancinmu da su kenan? Za mu zama irinsu kenan.”

A nan ne Jagora (H) ya yi kira ga ‘yan uwa akan inganta dabi’u da cewa: “Dole ne a ga cewa dabi’armu mu ya bambanta ne (da na sauran mutane), ya zama mun yi kama da abin da muke kira a kai, ta nan ne wanda duk ya shigo cikinmu sai ya zama kamar daidai da mu. Haka nan abin na yaduwa har al’amari ya yi karfi, har kuma yazuwa lokacin da Allah Ta’ala zai kawo nasara.”

Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa: “Ba dabara ba ne. Za a koma ga Allah ne, Allah ne ke yin abin nan. A bida a wajenSa. Kar a yi wasa da sallar dare, kar a yi wasa da karatun Alkur’ani. Kar a yi wasa da addu’o’i Ma’athurai. Ga Ramadan ya zo ya wuce; makarantar taqawa… Yanzu kuma mutum ya kara kaimi, har izuwa lokacin in Allah Ya nuna masa wani Ramadan din sai ya kara shiri. Wannan dama aka bamu, domin daidai wannan lokacin ka dawo ka kusanci Allah Ta’ala. To kuma sai ka mike haka nan, ba kuma ka yi nesa da Shi (SWT) bayan watan ba.” 

Jagora ya kara kira ga ‘yan uwa da su kasance masu sadaukarwa da dauriya, sannan kuma su jure ma jarabawar da za a fuskance su da ita na cutarwar azzalumai. Yace: “Za ka ci jarabawar ne ta hanyar dauriya. Bilhasali ma, muna iya cewa Aljanna ma ladan dauriya ne.”

Shaikh Zakzaky ya jaddada manufar da’awar da yake yi, cewa kira ne zuwa ga tabbatar da addinin Musulunci a wannan nahiyar. Inda yace ba kira ne zuwa ga wata Mazhaba ba. “Ka ga wannan fikira din, cewa da’awa ce Mazhabiyya (za a yi) hadari ne babba. Ba da’awa Mazhabiyyah ba ce! Ko da aka yi juyin juya hali a Iran, ba da’awa Mazhabiyya ba ce, addinin Musulunci aka ce. Su Mazhabobi suna cikin addini ne. Wanda duk ya ce da’awar wani bangare ne yake yi, to shi kenan, bangarancin na shi zai yi.”

Ya cigaba da cewa: “Tun farko ba mu dauke shi a matsayin cewa muna da’awa ne na wata mazhaba ba. Kuma ba mun cewa mutane mun kawo musu wani sabon addini ba ne, kuma ba mu ma ce musu ma dole ne lazim sai mutum ya Musulunta ne sannan nizamin Musulunci zai yi aiki ba. Ko a da, lokacin da addini ya kafu a lokacin Annabi ba kowa ya zama Musulmi ba, ba a kuma ce sai kowa ya zama ba. Amma addinin ya kafu. Kuma lokacin Shehu Usman Danfodiyo addinin nan ya kafu, amma ba kowa ne ya zama Musulmi ba. Amma kuma ba a ce sai kowa ya zama Musulmi ba, amma addinin Musulunci ke iko.”

Yace: “To mu muna batun shi addinin ya yi iko ne. Shi kuma ikon addinin abinda yake nufi shi ne, ba za a saba ma ka’idar addinin ba ne, shi addinin shi ne (zai zama) a sama. Abin da yake nufi ke nan.” 

Jagoran yace: “To su kuma mutane wannan ya shige musu duhu saboda ana ta yi musu da’awar bangaranci. Wani ya dauki abu ya ce su ‘yan darika kaza ne, ko su ‘yan kungiya kaza ne, sai ya zama shi kungiyancin ne ma kamar ya zama addinin a wajen mutane. Tunda su kungiya shi ne addini a wurin su, sai suka dauka mu ma kungiya din ne. Mu kuma mukan ce, mu ba kungiya ba ce, ballantana ku kalle mu ta wannan fuskar. Amma sun na ce, ala dole yadda suke kallon kan su, haka za su kalle mu. Saboda haka ne tunda su sun ba kansu suna, dole ne su ba mu suna mu ma. Mun ki ko mun so”

Yace: “Haka ne yasa ka ga a kasar nan, da zaran mutum ya fara magana, sai a ce, dan mene ne? Sai a ce, dan kaza ne. Shi ke nan. Dan kaza, Dan kaza, Dan kaza. Kowa ya zama dan wani abu. Ka rasa wane ne Dan Musulunci? Yaushe ne kuma za a samu Dan Dusulunci? Yaushe za a samu mutane su ce mu Musulmi ne? Illa iyaka. A’a, sam wannan ba abin da ya damu wadansu ba ne.”

A karshen jawabinsa, Jagora (H) ya sake jaddda ma ‘yan uwa cewa lazim in har mutum zai yi addini, to sai ya fuskanci jarabawa daga azzalumai. “Nakan ce, in da za a ce wani ya yi addini, sai ya yi nasara ba tare da ya sha wahala ba, sai muce, kai! wannan lallai kana da gatanci a wajen Allah. Wannan ma kila gatancinka ma ya fi na Annabi (S), don shi Annabi (S) ya sha wahala. Kuma shi ne me cewa; ‘manya-manyan darajoji suna tare da manya-manyan bala’o’i’ Yace; ‘daidai gwargwadon darajar mutum daidai gwargwadon bala’in da za a saka mashi.’ Yace; ‘tunda Annabawa suka fi daraja, su suka fi shan wahala, kuma tunda shi ne babbansu, to shi ya fi kowanne shan wahala’

“To da akwai wata hanya da ba hanyar wannan wahalan ba, da an ba Annabi (S). Don haka, wanda duk yake rudan kansa cewa, yanzu zai bi wata hanya ce tubus-tubus ba wata wahala, lafiya lau sai addini ya tabbata, to yana rudan kansa ne. Wannan hanyar ta jarabawar, itace kadai kwara daya. Kuma alkawarin Allah ne nasara insha Allah. Saboda haka, muna fata Allah Ta’ala ya raya zukatanmu da tarbiyan wannan addini, kuma Ya datar da mu da katar, ya kuma tabbatar da zukatanmu da duga-duginmu, har yazuwa ga nasara insha Allahu ko karewan wa’adinmu.” Ya kammala.

@SZakzakyOffice
#FreePalestine 
#PrayForPalestine 
#OurMartyrsOurHeroes 
#internationalconference 
13/04/2025

Post a Comment

Previous Post Next Post