Jagora (H) Ya Gudanar Da ‘Ranar Taklif’ Ga Yara A Abuja

Daga Ofishin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)

Da safiyar Asabar 16 ga Sha’aban 1446 (15/2/2025) Jagoran Harkar Musulunci Shaikh Ibraheem Zakzaky ya gana da kananan yara maza da mata wadanda suka cika shekarun Takhlifi a gidansa da ke Abuja.

Jagoran ya fara da taya yaran murna da kaiwa shekarun Takalifi, inda yace wannan ni’ima ce daga Allah Ta’ala da ya samar da su daga rashi zuwa akwai. “A samar da mutum daga rashi, da baka, aka haife ka, ka ga ni’ima ce yinka da Allah Ya yi.”

Yace: “Bayan samar da kai daga rashi, sai Allah Ta’ala kuma Ya yi ka a mutum. Wannan babban daraja ce a yi ka a mutum, domin za ka ga akwai halittu iri-iri da aka yi, irin su dabbobi, tsuntsaye, da kwari, wasu masu tafiya fa kafafu, wasu masu jan ciki, wasu masu tashi, halittu daban-daban. Duk su ma halittan Allah ne da Ya ga damar ya yi su.” Yace: “Amma sai Allah Ya yi ka a mutum wanda ya fifita birbishin duk wadannan.”


Ya cigaba da cewa: “Banda wannan Allah Ta’ala Ya halicci Mala’iku, ya halicci kuma Aljannu, su ma halittu ne masu rai. Amma su mutane sun bambanta, na cewa su an yi musu halitta ne na daban, na cewa an kawo su ne gidan gwaji, za a gwada su ne a ga wa zai yi aiki mai kyau. Ka san kuwa in mutum bai yi aiki mai kyau ba, kila zai yi mare kyau.”

Da yake bayani ga yaran akan nauyin da ya hau kansu, Shaikh Zakzaky ya bayyana musu yadda Allah Ta’ala ke dauke alkalami ga yaro kafin ya cika shekarun Takhalifi, zuwa yadda za a fara rubuta masa lada da zunubi akan kowane aiki idan ya yi. 

Yace: “Allah Ta’ala Yana dauke alkalami ga yaro har sai ya shiga shekarun Takalifi, lokacin ne za a gwada shi. In aka haifi yaro aka koyar da shi addini, in ya yi aikin kirki, ya yi sallah, ko ya yi azumi, ko ya yi sadaka, ko ya sa da zumunci ya gaishe da ‘yan uwansa, ko ya kyautatama wani, ko ya yi tsinutuwa ya mayar ga mai shi, to duk za a rubuta masa lada. Amma in bai yi sallah ba, ko bai yi azumi ba misali, to ba za a rubuta masa zunubi ba, ya dai rasa lada ne a lokacin.

“To amma in ya kai shekaran da ake ce masa yanzu Baligi ne shi, to ya cika shekarun Takalifi kenan. Ma’anar Takhlifi shi ne kallafawa, wato tilastawa dole. In mutum ya kai shekarun Takhlif ya kai shekaran da za a saka masahi ya yi dole. Ma’anar dole a nan ba bulala za a saka masa ace ya yi kaza ba, amma a rubuce an ce masa dole ya yi. In ya ki yi, yana da zunubi, in ya yi yana da lada. Alhali a da kafin ya kai Taklifin in ya yi yana da lada, in bai yi ba, yana da zunubi.”


Jagora ya jaddada kira ga yaran akan su san nauyin da ya hau kansu a yanzu na shari’a, don haka su lizimci sauke wajibai, kamar sallah da azumi da sauran ibadu, tare da nisantan aikata Haramun.

Bayan sallar nafila raka’a biyu da Jagoran ya ja yaran don koya musu yadda ake sallah, ya kuma karkare da musu addu’ar Allah Ya kyautata rayuwarsu da tarbiyarsu, ya sa su kasance mataimaka ga Sahibul Asr waz Zaman (AS). Sannan ya yi musu fata da cewa: “Duk cikanku insha Allah za a yi tsawon rai kuma a yi aiki mai kyau, a karbi satifiket mai kyau a karshen rayuwa.”

@SZakzakyOffice
#Taklif1446 
#ShaabanKareem 
#PrayForPalestine 
#OurMartyrsOurHeroes 
16/Shaaban/1446
15/02/2025

Post a Comment

Previous Post Next Post