CUTAR ‘TYPHOID’ - Tare Da MLS Abduljalal muhammad



Yau akalarmu zai juya ne akan matsalar  Cutar typhoid (TYPHOID FEVER). Ya za mu duba mene ne ‘typhoid’ sannan ya ake samun shi sannan ya zamu yi maganin shi kuma ya zamu kare kanmu daga kamuwa da shi. Da farko dai ‘typhoid’ wata kwayar cuta ce wanda ake kiran ta da (SALMONELLA TYPHI) a turance. Ita wannan kwayar  cutar tana yaduwa ne bayan ta shiga jikin mutum sannan da ta shiga za ta fara rarrabuwa a cikin jinin mutum daga nan sai alamu ya fara bayyana a jikin mutum. Sannan babban inda tafi kamawa a jikin mutum shi ne karamin hanji (SMALL INTESTINE) daga nan sai alamunta ya bayyana. 

ALAMOMIN CIWO TYPHOID 

Ita kwayar cutar typhoid tana zama ne kawai a jikin mutum banda sauran halitta.  Alamomin ta sun hada da:

1. Zazzabi mai zafi (high fever).

2. Tashin zuciya (nausea).

3. Ciwon cikin (abdominal pain).

4. Ciwon Kai (headache). 

5. Gudawa (diarrhoea). 

Wadannan sune kadan daga cikin alamomin cutar

ana iya tabbatar  da cutar ne ta hanyan gwaji na jini (blood test).

Hanyoyin kamuwa da cutar sun hada da:

1. Rashin tsafta ce abincin mu, misali a duk lokacin da za mu dafa  abinci to wajibi ne mu tsafta ce abin dafawar a naso duk abin da za a dafa to a wanke shi da gishiri sosai. Kokuma ganye da muke ta’ammuli da su kamar kabeji,   alayyahu da sauransu, to ana so kafin a yi amfani da su ya zama a wanke sosai. 

2. Shan ruwan sha mara tsafta. Wannanma wani babban dalili ne da yake haifar da cutar saboda akwai kwayoyin cutukan a jikin ruwa mara kyau to wajibi ne mu tabbatar da tsaftar ruwan shan mu kafin mu sha. Ana tsaftace ruwa ne ta hanyar tacewa ko kuma sanya alum a ciki yanda ake tace ruwa shi ne za a dafa ruwan ne sai ya tafasa sannan a sauke a barshi ya yi sanyi to a wannan lokacin ana sa ran duk wata kwayar cuta dake ciki ta mutu.

3. Rashin tsaftar gida: wannan ma babban dalili ne dake taimakama cutar. Wajibi ne mu rinka tsaftace kwayar gidajenmu da kuma makewayinmu sannan mutabbatar da cewa kwatar gida bashi kusa da rijiya saboda akwai abin da akikira UNDER GROUND CONNECTION shi ne yaduwar kwata ko makewayi da rijiya ta kasa tabbas suna haduwa indai ba ai ba su tazara ba. Dole a kiyaye hakan ya zama ba a wanke wanke a kusa da rijiya sannan an bayarda 20metters tsakanin rijiya da makewayi.

HANYOYIN DA ZAMU KARE KANMU DA KAMUWA 

1: wanke hannu kafin cin abinci kuma a tabbatar da ya wanki.

2: wanke abinda za a sa abincin kafin a sanya

3: tabbatar da tsaftar jiki da na muhalli

4: tabbatar da tsaftar ruwan sha da wanda ake girki dashi

5 garzayawa asibiti da zaran an ji wata alama tunkafin ya tsananta

Post a Comment

Previous Post Next Post