An Gudanar Da Jana’izar Kareemah Bukhari Mustafa Sambo

 


INNA LILLAHI WA INNA LILLAHI RAJI'UN. 

An gudanar da jana’izan Kareemah Sambo a ranar Talata 14 /1/2025 kamar yadda addinin musulunci ya tanada a garin Karbala dake ƙasar Iraqi. Jana’izar ta gudana ne da yammacin wannan rana. 

Kafin a yi jana'izan an kai ta cikin haramin Imam Hussain (AS) inda aka yi addu’o'i sannan aka kai ta ziyarar Haramin Abul Fadalul Abbas (A S). 

Kareemah Sambo ta rasu ne a ranar Litinin 12 ga watan Rajab hijira 1446 wanda ya yi daidai da 14 ga watan 1 miladiyya.  

An haifi Kareemah Sambo a ranar 1 ga watan Ramadan hijira na (1445) wanda ya yi daidai da 12 ga watan 2 a shekarar 2024 miladiyya. 

 Amincin Allah ya tabbata a gare ki ranar da aka haife ki da ranar da ki ka rasu da ranar da za a tashe ki.

Post a Comment

Previous Post Next Post