Daga Mardiyya Kabiru
A ranar Litinin 20/01/2025 ‘yan'uwa
musulmi almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) dake Garin Bomo, suka gudanar da addu'ar
bakwai na Kareema Sambo a muhallin Fudiyyah Bomo.
Bayan saukan karatun Alkur'ani mai
girma da aka gudanar an kara da mashahuran addu’o’i duk hadiya zuwa ga Marigayiya
Khareemat. Daga nan aka karanta addu'ar
ziyarar Imam Hussain (A.S) sai Du’a Tawassul.
Allah ya jibanci Marigayiyah
Khareemat ya sada ta da masoyanta A’immatu Ahlul baiti (AS).
-MEDIA FORUM BOMO
Post a Comment