Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai. (Daga cikin muminai akwai mazaje na kwarai kan abin da suka yi wa Allah alkawari. Daga cikinsu akwai wanda ya cika alkawarinsa, kuma daga cikinsu akwai wanda yake jira (lokaci), kuma ba su sauya ba ko kadan daga alkawarinsu.
Cikin bakin ciki muka samu labarin shahadar Shehin Malami Hujjatul Islam da Musulmi Sayyed Hassan Nasrallah tare da wasu gungun 'yan'uwansa a cikin gwagwarmayar da suke yi a Lebanon mai daraja, da kuma gomman fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba da aka rutsa a wannan mummunan kisan kiyashi da sojojin maƙiya Allah na Isra'ila suka yi a ƙauyen Beirut.
Wannan Babban shahidi ya kasance abin koyi ne na jagoranci wanda ba a taba yin irinsa ba a shekarun baya-bayan nan. Ya taka rawar gani sosai wajen 'yantar da yankunan Lebanon daga mamayar da Isra'ila ta yi, sannan ya kuma tallafa wa Iraqawa da duk wani abin da zai iya wajen kwato kasarsu daga 'yan ta'addar ISIS. Ya kuma dauki babban matsaya wajen tallafawa al'ummar Palastinu da ake zalunta har sai da ya biya da rayuwarsa mai kima.
A yayin da muke mika sakon ta'aziyyarmu da alhinin mu ga al'ummar kasar Lebanon masu girma da daukacin al'ummar da ake zalunta cikin wannan babban rashi da kuma babban jarabawa da ya same mu, muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya jikan marigayin da rahama da jin kai ya kuma sada shi da abin kaunarsa mai tsarki Annabi Muhammad da iyalan gidansa tsarkaka a madaukakiyar aljannah, ya kuma sanya hakuri da sanyin zuciya da juriya ga iyalansa da duk masoyansa. Daga Allah mu ke kuma gare Shi za mu koma.
(24 / Rabi` al-Awwal / 1446 AH) daidai da (28/9/2024 AD)
Ofishin Sayyid al-Sistani - Najaf al-Ashraf
Jawabin da Jagoran juyin juya halin Musulunci Imam Khamenei ya fitar dangane da shahadar Babban Sakataren Kungiyar Hizbullah Hujjat Al-Islam Wal-Muslimeen mai daraja Sayyed Hasan Nasrallah:
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai. Ga Allah muke kuma zuwa gare Shi za mu koma. Ya ku al'ummar Iran. Ya ku al'ummar Musulunci masu girma. Babban mujahid, mai fafutukar tsayin daka a wannan yanki, malamin addini nagari, kuma kwararre a fagen siyasa, Sayyid Hasan Nasrallah, Allah ya kara masa yarda, ya samu lambar yabo ta shahada sakamakon harin da aka kai da maraice a kasar Lebanon.
Jagoran gwagwarmaya ya samu ladan jihadi na tsawon shekaru da dama da ya jagoranta saboda Allah, kuma ya yi juriya dangane da wahalhalun da ya sha a lokacin wannan yaki domin Allah. Ya yi shahada a lokacin da ya shagaltuwa da shirin kare mutanen yankin Beirut, gidajensu da aka lalata, da 'yan uwansu da aka raba su da su, kamar yadda ya kwashe shekaru da dama yana gwagwarmayar kare al'ummar Palastinu da aka yi wa zalunci da danniya, yana kare garuruwa da kauyukan da aka kwace, da gidajen da aka lalata, da kuma 'yan uwansu wadanda aka rika yi wa kisan kiyashi.... Samun darajar shahada ita ce haqqin da ya kamata ya samu bayan duk wannan jihadin da ya yi.
Duniyar Musulunci ta yi asarar mutum mai dattako da mutunci, kungiyoyin gwagwarmaya a duniya sun yi rashin wani fitaccen mai rike da tuta, kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon kuma ta yi rashin shugaba jarumi mara tamka, amma albarkar dashen da ya gina da ayyukansa da kokarinsa na tsawon shekaru da dama ba za su taba gushewa ba. Harsashin da ya aza a kasar Lebanon, wanda kuma ta hanyarsa ne ya rika jagorantar sauran cibiyoyin gwagwarmaya, ba zai rushe ba saboda rashinsa kadai ba, hakan ma zai kara karfi da karfe ne albarkarcin jininsa da na dukkanin shahidai da aka zubar. Kuma hare-haren da za a kai a gaba a kan rugujajjiyar jikin sahyoniyawa za su kara zafafafa, kuma da yardar Allah da ikonsa, za a fuskanci rukushi da durkushewa.
Mugun son kai na sahyoniyawan bai cimma nasara ba a cikin wannan lamari, domin kuwa jagoran gwagwarmaya ba wai mutum ne kawai ba, a'a fikira ce da kuma makaranta, kuma wannan hanya za ta ci gaba. Kamar yadda jinin shahidi Abbas Al-Moussawi bai kasance a banza ba, haka ma jinin shahidi Hassan ba zai zama banza ba.
Ina mika ta'aziyyata da taya murna ga wannan mahaifi mai girma, da kuma Uwargidan wannan Shahidi mai girma, wadda ita ma a baya ta sadaukar da danta Sayyeed Hadi, saboda Allah, da kuma 'ya'yanta masu albarka, da iyalan shahidai a cikin wannan lamari.
Haka kuma ga kowanne mutum a cikin kungiyar Hizbullah, da kuma manyan jami'ai a kasar Lebanon, da dukkanin bangarorin gwagwarmayar, da kafatanin al'ummar musulmi, dangane da shahadar Nasrallah mai girma da 'yan uwansa. Sannan na ayyana kwanaki biyar na zaman makoki a kasar Iran. Ina rokon Allah ya sada shi da waliyyansa.
Amincin Allah ya tabbata ga bayin Allah salihai
Sayyed Ali Khamenei | 09/28/2024
Post a Comment