Daga Karbala ƙasar Iraq, an gabatar da jana'izar ɗaya daga cikin ɗalibai Mata almjiran Sayyid Zakzaky (H) da Allah ya yi wa rasuwa a ranar Talata 1 ga watan Oktoban 2024, inda aka yi jana'izarta ranar Laraba 02/10/2024.
Marhuma Fatima, dai Mata ce ga Malam Ahmad Sani, ta rasu ne 'yan kwanaki da haihuwa, inda a ranar Laraba daga Haramin Imam Hussain (A.S) aka yi mata jana'iza bayan kwashe awanni ana karatuttuka da ziyarori tsakanin Haramin na Imam Hussain (A.S) da Abul Fadhlul Abbas daga ƙarshe aka wuce da ita makwancinta na ƙarshe.
‘Yan'uwa ɗalibai Maza da Mata da ke karatu a garin na Karbala ne suka halarci jana'izarta da yi mata rakiya zuwa makwancinta cikin jimami da juyayi.
Post a Comment