Jagora Shaikh Ibraheem Ya’qoub Zakzaky (H) ya gabatar da muhimmin jawabi a wajen taron ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar Shahidi Jagora Ayatullah Sayyid Ali Khamenei (Rahimahullah), mai taken “Cell No. 14”, wanda aka fassara zuwa harsuna daban-daban ciki har da Hausa, Jamusanci da Kazakh.
An gudanar da taron ne a birnin Tehran na Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A cikin jawabinsa, Jagora Sayyid Zakzaky (H) ya yi bayani kan muhimmancin yaɗa ilimi da tarihin gwagwarmayar shugabanni masu fafutuka, yana mai bayyana yadda irin waɗannan littattafai ke taimakawa wajen wayar da kan al’umma da kuma ƙarfafa ruhin juriya, sadaukarwa da neman adalci.
Fassarar littafin zuwa harshen Hausa, mai taken “Haƙuri Na Tare Da Nasara”, na daga cikin manyan matakan da za su bai wa al’ummar Hausawa damar fahimtar rayuwar Shahidi Jagora Sayyid Ali Khamenei da irin ƙalubalen da ya fuskanta, tare da darussan gwagwarmaya da ke ƙunshe a cikin rayuwarsa.
Taron ya samu halartar manyan malamai, masana da baƙi daga ƙasashe daban-daban, inda aka tattauna kan muhimmancin fassara littattafai masu amfani zuwa harsunan duniya domin ƙarfafa fahimtar juna da kuma yaɗa ilimi tsakanin al’umma.

Post a Comment